Al-Bashir Ya Kori Ministan Harakokin wajen Kasarsa
Shugaba Omar Al-Bashir na kasar Sudan ya sauke Ibrahim Ghandour ministan harakokin wajen kasar daga kan mikaminsa
Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya alhamis, gwamnatin kasar Sudan ta sanar da sauke Ibrahim Ghandour ministan harakokin wajen kasar daga kan mikaminsa.
Kafin hakan dai, an kwashe watani da dama ana rade-radin korar ministan daga cikin gwamnati.
Duk da cewa gwamnatin ta Sudan, ba ta bayyana dalilin korar ministan ba, to amma a ranar Larabar da ta gabata, ministan ya fito fili ya bayyana cewa hukumomin birnin Khartoum na fama da matsalar rashin kudi, da hakan ya sanya ta kwashe watani ba tare da biyan albashin ma'aikatanta dake ketare ba, da kuma kasa rashin biyan kudin haya na wasu ma'aikatun jakadancin kasar dake kasashen ketare.
Ibrahim Ghandour da ya kasance Likitan hakori ya karbi jagorancin ma'aikatar harakokin wajen kasar ta Sudan a shekarar 2015.