Zimbabwe : Majalisa Za Ta Saurari Mugabe Kan Batan Kudin Lu'u-Lu'u
A Zimbabwe, kwamitin majalisar dokokin kasar mai kula da harkokin ma'adunai da makamashi, ya bukaci tsohon shugaban kasar Robert Bugabe da ya yi bayyani kan salwantar wasu kudade rara na lu'u-lu'u da yawansu ya kai Dalar Amurka Bilyan 15.
A ranar 9 ga watan Mayu mai zuwa ne, ake sa ran majalisar dokokin kasar zata saurari Mista Mugabe, kan badakalar batan kudaden, kamar yadda shugaban kwamitin Temba Mliswa ya shaida wa manema labarai.
Shi dai Mugabe ya bayyana a yayin bikin cika shekarunsa 92 a duniya, cewa akwai kamfanonin da suka shafe shekaru da dama suna bidar lu'u-lu'u a cikin kasar ba tare samar wa kasar wata riba ba.
Wasu bayyanai na daban sun ce ko baya ga tsohon shugaban kasar, za'a saurari tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar, Joice Mujuru, saboda bankado sunanta a cikin badakalar ta batan kudaden Lu'u-Lu'un.