Babu Hadin Kai Tsakanin Kasashen Afrika-Shugaban Kasar Guinea
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30164-babu_hadin_kai_tsakanin_kasashen_afrika_shugaban_kasar_guinea
Shugaban kasar Equatorial Guinea ya bayyana damuwarsa da rashin hadin kai dake tsakanin kasashen Afrika
(last modified 2018-08-22T07:01:44+00:00 )
Apr 21, 2018 14:34 UTC
  • Babu Hadin Kai Tsakanin Kasashen Afrika-Shugaban Kasar Guinea

Shugaban kasar Equatorial Guinea ya bayyana damuwarsa da rashin hadin kai dake tsakanin kasashen Afrika

Kamfanin dillancin Labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Shugaba Teodoro Obiang yana fadar haka a safiyar yau Asabar. Ya kuma kara da cewa kekyawar misali shine yadda yan wasu kasashen Afrika suke da hannu dumu-dumu a yunkurin juyin mulkin da bai sami nasara ba a kasar a watannin da suka gabata.

A cikin watan Decemban shekara ta 2017 ne jami'an tsaro na kasar kamaru suka kama mutane fiya da 30 a kan iyakar kasar da kasar equaterial guinea , wasu wadanda aka kama sun fito ne daga kasar Chadi, wasu kuma daga kasar Sudan sannan wasunsu daga Afrika ta tsakiya, suna dauke da manya manyan makamai suna nufin shiga kasar ta Equatorial Guine a lokacinda Jami'an tsaron kasar ta Kamaru suka kamasu su.  Shugaba Obiang ya ce har yanzu bai fahinci manufar wadannan mutane da yunkurin juyin mulki a kasarsa ba. 

Bayan kama mutanen a kan iyakar kasar da kasar Kamaru ne gwamnatin kasar ta Equatorial Guinea ta bada sanarwan cewa ta gano wani yunkurin juyin mulki a kasar. Har'ila yau ana zargin wasu turawa suna da hannun a cikin yunkurin juyin mulkin.  daga ciki akwai Mark Thatcher dan Magrate Thercher tsohuwar Priministan kasar Britania