Mauritaniya : 'Yan Adawa Zasu Shiga Zabe, Bayan Shekaru 10 Na Kauracewa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30216-mauritaniya_'yan_adawa_zasu_shiga_zabe_bayan_shekaru_10_na_kauracewa
Gungun jam'iyyun da ake kira masu tsananin adawa a Mauritaniya, sun bayyana aniyarsu ta shiga zabukan kasar dake tafe.
(last modified 2018-08-22T07:01:44+00:00 )
Apr 23, 2018 06:40 UTC
  • Mauritaniya : 'Yan Adawa Zasu Shiga Zabe, Bayan Shekaru 10 Na Kauracewa

Gungun jam'iyyun da ake kira masu tsananin adawa a Mauritaniya, sun bayyana aniyarsu ta shiga zabukan kasar dake tafe.

'Yan adawan dai sun zau shiga zabukan da suka hada dana wakilan jihohi da kuma na shugaban kasa na 2018 da 2019, bayan kauracewa zabukan na tsawan shekaru goma.

Kakakin 'yan adawan Mohamed Ould Maouloud, ya shida wa masu aiko da rahotanni cewa, wannan babban ci gaba a tarihin kasar.

A watan Nowanba na 2018 ne za'a gudanar da zaben wakilan jihohi, sai kuma na shugaban kasa a watan Afrilu na 2019.

Shugaban kasar Mohamed Ould Abdel Aziz, baya daga cikin wandanda zasu fafata a zaben, kasancewar ya kammala wa'adin shugabancinsa a karo na biyu.