Amurka Na Shirin Gina Wani Sansanin Sojojinta A Nijar
Kafafen watsa labaran Amurka sun ba da labarin cewa Amurkan tana shirin gina wani sansanin jiragen saman yakinta marasa matuka a kasar Nijar don amfani da wajen wajen fada da kungiyoyin ta'addanci.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ba da rahoton cewa sojojin Amurka a Nijar suna shirin gina wani sabon sansanin jiragen saman yaki marasa matuka a Nijar din da ake sa ran za a fara aiki da shi a farko-farkon shekara ta 2019, don abin da suka kira kai hare-hare kan kungiyoyin ta'addanci.
Rahoton ya jiyo wasu jami'an Amurkan suna cewa gina sabon sansanin ya biyo bayan bukatar hakan ne da gwamnatin Nijar ta gabatar sannan kuma za a gina shi ne a jihar Agadaz.
Bayanai sun ce daga lokacin da aka gama gina sansanin, Amurkawan za su mayar da jiragen yakinsu marasa matuka samfurin MQ 9 da a halin yanzu suke sansanin sojin na su da ke birnin Yamai. Sai dai Amurkawan ba su yi karin bayani kan yawan jiragen da za a jibge a sabon sansanin da kuma yawan sojojin da za a jibge su a wajen ba.