Najeriya: An Kashe Karin Mutane 11 A Jahar Benue
Gwamnatin jihar Benue ta ce akalla mutane 11 sun rasa rayukansu a garin Makurdi da ke jihar, bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a baya bayan nan.
Harin yazo ne kwana guda bayanda wasu ‘yan bindigar suka hallaka mutane 18 a harin da suka kai kan wata mujami’a.
Kamfanin dillancin labaran faransa AFP ya nakalato Rilwanu Adamu, mai bai wa gwamnan jihar Benue shawara akan addinin Musulunci na cewa an kai harin na baya bayan nan ne akan Hausawa ‘yan kasuwa da ke birnin Makurdi.
Adamu ya ce bayaga mutane sha daya da suka rasa rayukansu akwai wasu biyar na daban da aka jikkata sannan kuma a yiwa 'yan kasuwa hasara mai yawa bayan da aka kona masallatai biyu a harin dake zaton na daukan fansa ne,
A jiya laraba ce daruruwan mutane suka gudanar da zanga-zanga a garin Makurdi domin nuna bacin rai bisa rasa rayukan jama’a da ake ci gaba da fuskanta, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da ake dagantawa da makiyaya.
Har ila yau a jiya Laraba majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci shugaban kasar Muhammadu buhari don bayyana a gabanta, saboda yadda ake samun hasarar rayuka a jihar Benue da sauran sassan kasar.
Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bukaci da sauke dukkanin manyan hafsoshin sojin kasar da ma manyan jami'an tsaro sauran bangarorin, bisa a bin da suka kira kasa tabbatar da tsaro ga 'yan Najeriya.