Najeriya : An Tabbatar da Sace Soja
Hukumomin sojin Nijeriya sun bayyana a Lahadi nan cewa, wasu dauke da makamai da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da wani babban jami'in soji na kasar a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.
Kakakkin sojin Najeriya kanal Usman Abdul ya shaida wa manema labarai cewa, a ranar 26 ga wata da misali karfe 7 da rabi na yamma, an yi garkuwa da kanal Samaila Inusa a yankin Kamazo Chikkun da ke jihar.
Inusa, wanda ya yi aiki a kwalejin horar da sojoji, an yi awon gaba da shi tare da matarsa a jihar Kaduwa.
Kakakin ya ce, an saki matar mista Inusa, sannan suka wuce da Inusa cikin motarsu zuwa birnin Abuja babban birnin kasar.
Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin wannan lamari ko neman kudin fansa.