DRC : An Yanke Wa Jagoran 'Yan Tawaye Daurin Shekaru 20
Wata kotun soji a Jamhuriya Demukuradiyyar Conko, ta yanke hukuncin daurin shekaru ashirin a gidan kaso ga wani madugun 'yan tawaye, bisa samunsa da laifukan yaki a shekaru goma da suka gabata.
Maro Ntumwa da aka fi sani da '' Le Marocain'' an same shi da laifukan da suka hada da fyade, da bautar wa ta hanyar lalata da kuma hare hare kan fararen hula a gabashin kasar.
A cewar kungiyar Rial International, Ntumwa, ya gallazawa daririwan 'yan kauye a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007, ta hanyar garkuwa da maza da mata da daure su jikin bishiyoyi ko jefasu cikin ramuka.
Kotun sojin ta kuma bukaci madugun 'yan tawayen da ya biya diyya data kama daga Dalar AMurka 2,000 zuwa 5000 ga ko wanne mutum daga cikin wadanda aka ci wa zarafin.
Yankin arewa da kudancin Kivu na RDC, ya dai yi fama da rikice rikice da ya hada dana da mayaka dake kwatar kudade ga fararen hulda ko kuma suke fada domin mallakar wurare masu arzikin karkashin kasa.