Shugabannin Afrika Na Taro Don Ceto Tafkin Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30412-shugabannin_afrika_na_taro_don_ceto_tafkin_congo
Kimanin shugabannin kasashe dana gwamnatocin Afrika 20 ne suka hadu a Brazaville, babban birnin Congo Brazaville, a wani taro mai manufar ceto tafkin Congo.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 29, 2018 11:01 UTC
  • Shugabannin Afrika Na Taro Don Ceto Tafkin Congo

Kimanin shugabannin kasashe dana gwamnatocin Afrika 20 ne suka hadu a Brazaville, babban birnin Congo Brazaville, a wani taro mai manufar ceto tafkin Congo.

Taron wanda shi ne irinsa na farko da ya hada shuwagabanni da gwamnatoci daga kasashen yammaci da tsakiyar nahiyar, na da manufar yin nazari kan hanyoyin kare tafkin na Congo.

Shi dai tafkin Congo ya kunshi daji mai yanayin zafi na biyu mafi girma a duniya bayan Amazonia, wanda kuma bayan hakan ya kunshi halliti irin na namun daji da tsutsaye da tsirai da kuma kifaye iri daban daban, a cewar kungiyar Greenpeace.

Kungiyoyin kara muhalli dai sun soki wani matakin gwamnatin Congon, na bada lasisin aiki ga wasu kamfanonin China a dajin.

A shekaru biyu da suka gabata an dai ware kudade da yawan su ya kai Bilyan uku na Yuro  domin kare albarkatun ruwan tafkin da kuma dakatar da sare-sare itatuwa, ta hanyar bunkasa wasu ayyukan tattalin arziki masu daurewa ciki har da yawan bude ido.