Har Yanzu Akwai Fargabar Yiwuwar kai Harin Ta'addanci A Arewacin Burkina Faso
(last modified Wed, 02 May 2018 17:45:45 GMT )
May 02, 2018 17:45 UTC
  • Har Yanzu Akwai Fargabar Yiwuwar kai Harin Ta'addanci A Arewacin Burkina Faso

Ma'aikata a bangaren shari'a a garin Djibo da ke cikin lardin Soum a arewacin kasar Burkina Faso, sun kaurace ma wuraren ayyukansu saboda fargabar yiwuwar kai hare-haren ta'addanci a garin.

Jaridar Lomond ta kasar Faransa ta bayar da rahoton cewa, ma'aikatan kotuna da sauran bangarori na shari'a a garin Djibo sun gudu sun bar wuraren ayyukansu ne bayan samun wasu bayanai, da suke nuni da cewa 'yan ta'adda na shirin kaddamar da hare-hare na daukar fansa musamman a kan ma'aikatan shari'a.

Daga cikin ma'aikatan da suke gudu daga bakin aikinsu har da manyan alkalai guda 6, da kuma masu shigar da kara 8 gami da sauran ma'aikata, inda a halin yanzu kotuna suke gaba da zama a rufe a yankin tun daga ranar 23 ga watan Afrilun da ya gabata., inda suka sha alwashin cewa ba za su koma bakin aikinsu ba har sai an tabbatar cikakken tsaro a yankin.