'Yan Bindiga Sun Sace Wani Bajamishe A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30536-'yan_bindiga_sun_sace_wani_bajamishe_a_somaliya
Kungiyar Agaji ta Red Cross ta sanar da sace jami'inta dan kasar Jamus a Magadushu babban birnin kasar Somaliya.
(last modified 2018-08-22T11:31:47+00:00 )
May 04, 2018 13:29 UTC
  • 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Bajamishe A Somaliya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta sanar da sace jami'inta dan kasar Jamus a Magadushu babban birnin kasar Somaliya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Daniel O'Malley shugaban kwamitin kungiyar agaji ta kasa da kasa wato Red Gross  a jiya alhamis na cewa wani gungun 'yan bindiga sun kai hari kan daya daga cikin hotel din jami'anta dake birnin Magadushu na kasar Somaliya.

Mista  O'Malley ya ce lamarin ya auku ne da daren larabar da ta gabata, inda 'yan bindigar suka yi awan gaba da daya daga cikin ma'aikatan kungiyar dan kasar Jamus.

Tun a  2012 ne kasar Somaliya ke fuskantar hare-haren ta'addanci daga  kungiyar  al-shabab wacce reshe ne na kungiyar alqaida.