An Soke Sabuwar Dokar Zabe A Kasar Madagaska
(last modified Fri, 04 May 2018 19:04:18 GMT )
May 04, 2018 19:04 UTC
  • An Soke Sabuwar Dokar Zabe A Kasar Madagaska

Kotun koli ta kundin tsarin mulki a kasar Madagaska ta suke wasu sassa na sabuwar dokar wacce majalisar dokokin kasar ta amince da ita wacce kuma ta jawo kace-nace a cikin yan siyasar kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ta bayyana cewa kotun koli ta kundin tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin soke wasu sassa na dokar ne don sun sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Kotun ta bayyana sassan da ta soke kamar haka, sashen mai gamaga kan sake irgen kuri'u, sashen sharuddan dan takarar shugaban kasa, amfani da akwatonan zane na musamman da kuma tsawo lokacin yakin neman zabe.

Tun ranar 21 ga watan Afrilun da ya gabata ne yan adawa suka fara zanga zangar nuna rashin amincewarsu da sabon dokar wacce suka ce tana nufin hana yan takara shugaban kasa na jam'iyyun hamayya shiga takarar shugaban kasa mai zuwa ne.

Ana saran a zaben shugaban kasa mai zuwa tsoffin shuwagabannin kasar ta madagaska, Maec Ravalomanana da kuma Andry Rajoelina duka zasu shiga takarar.