Burundi : An Dakatar Da Watsa Shirye Shiyen BBC Da VOA
Kasar Burundi, ta bada sanarwar dakatar da shirye shiryen gidajen radiyon muryar Amurka(VOA) da kuma BBC a kasar har na tsawon wata shida.
A sanarwar da shugaban majalisar sadarwa na kasar ya fitar a jiya Jumma'a, ya ce umurnin zai fara aiki daga ranar Litinin.
Mahukuntan Burindi dai na zargin muryar Amurka da BBC da karya dokokin kasar dangane da kafofin yada labaru, da kuma aikata ba daidai ba.
Haka nan majalisar ta kuma ja kunnen tashar Radiyo Fararansa (RFI), inda ta zargi tashar da yada labaran karya.
Wannan matakin na Burindi dai na zuwa ne makwonni biyu kafin zaben raba gardama kan daftarin yi wa kundin tsarin mulkin kasar, ciki har da a sashen kayyade wa'adin shugabancin kasar.
Kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa dai ta yi tir da matakin na dakatar da tashoshin biyu, wanda ta danganta da yunkurin gwamnatin Burundi na ci gaba da sanya takunkumi kan kafofin yada labarai.