Sudan:An Gabatar Da Shirin Karbar Makamai A Yankunan Da Ake Rikici
Mataimakin shugaban kasar Sudan ya tabbatar da ci gaba da shirin karbar makamai domin tabbatar da tsaro da sulhu a cikin kasar baki daya.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto Hassbu Muhammad Abdul Rahman mataimakin shugaban kasar Sudan na cewa za a ci gaba da shirin karbar makamai da aka mallaka ba kan ka'ida ba a yankunan da ake rikici, har sai an tabbatar da an karbe makaman baki daya, da kuma hakan shi zai tabbatar da tsaro da sulhu a fadin kasar gaba daya.
Yayin da yake ishara kan hasarar rayuka da mallakar makaman ba kan ka'ida ba ya janyo, Abdul Rahman ya ce a yayin da ya kai ziyara yankunan da ake rikici daga ciki har da yankin Darfur, ya gana da manbobin kwamitin koli da nauyin karbar makaman da aka mallaka ba kan ka'ida, sannan kuma ya gamsu da ayyukan da suke yi.
Kimanin shekara guda kenan da gwamnatin Sudan ta gabatar da shirin karbar makaman da aka mallaka ba kan ka'ida ba a yankunan da ake rikici, ciki kuwa har yankunan Darfur da Kurdufan ta kudu, da nufin tabbatar da tsaro tare da medo da kwanciyar hankali a fadin kasar gaba daya.