Masar: An Yankewa 'Yan Da'esh 9 Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada
Jaridar Yaumu Sabi'i ta Masar ta ce ayau litinin ne wata kotu ta yanke hukuncin zaman kurkukun na har abada ga mutane 9 sai kuma wasu mutane 2 da aka yankewa kowanensu zaman kurkuku na shekaru biyar
Babban mai shiga rda kara na kasar Masar Nabil Ahmad Sadiq, ya gabatar wa da kotun soja karar 'yan kungiyar Da'esh reshen Sinaa, bisa tuharmsu da kafa kananan kungiyoyin ta'addanci 43 sannan kuma da kai hare-hare har sau 63 da haddasa kisan yan sanda da kuma sojoji.
A cikin shekarun bayan nan kasar Masar tana fama da matsalar 'yan ta'adda masu alaka da kungiyoyin alka'ida da kuma Da'esh.
A yankin Sinaa mai iyaka da Palasdinu da kawai kungiyoyin masu dauke da makamai wadanda su ke kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar.
Daruruwan sojoji da 'yan sandan Masar ne su ka halaka da kuma jikkata sanadiyyar hare-haren.