An kashe 'yan ta'adda da dama a kasar Somaliya
Majiyar tsaron Somaliya ta sanar da kisan mayakan Ashabab da dama a kasar
Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Abdulkarim Husaini Gwamnan jihar Gamaldag na cewa cikin kwanakin hudu da su gabata Dakarun tsaron kasar tare da hadin gwiwar na kasashen Afirka sun kai sumame a sansanin mayakan Ashabab, inda suka hallaka Akalla 115 daga cikinsu, bayan kame wasu 110 na daban.
Abdulkarim Husain ya tabbatar da cewa sai a marecen jiya ne aka kawo karshen wannan gumurzu bayan da wasu 'yan ta'addar suka gudu zuwa cikin kauyukan jihar.
Yayin da yake jinjinawa Dakarun tsaron kasar, Gwamnan jihar Gamaldag ya ce duk matashin da ya meka kansa ga Dakarun tsaron kasar za a yi masa Afuwa.
Ya zuwa yanzu dai, kungiyar ta Ashabab ta yi asarar yankuna da dama dake kalkashin ikonta a kudu da tsakiyar kasar, saidai har hanzu ta na ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake a kan manya manyan jami'an Gwamnatin kasar musaman kan dakarun tabbatar da tsaro da Sulhu na kasashen Afirka Amisom.