Harin Ta'addanci Ya Hallaka Mutane 11 A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30686-harin_ta'addanci_ya_hallaka_mutane_11_a_somaliya
Jami'an 'yan sandar Somaliya sun sanar da mutuwa da kuma jikkatar mutane 21 sanadiyar tashin wani Bam a wata kasuwa dake cikin kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:48+00:00 )
May 10, 2018 06:24 UTC
  • Harin Ta'addanci Ya Hallaka Mutane 11 A Somaliya

Jami'an 'yan sandar Somaliya sun sanar da mutuwa da kuma jikkatar mutane 21 sanadiyar tashin wani Bam a wata kasuwa dake cikin kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto jami'an 'yan sandar Somaliya na cewa wani Bam ya tashi a wata kasuwa mai yawan cinkoson jama'a dake kudancin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 tare da jikkatar wasu 10 na daban.

Tuni dai Kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida ta dauki nauyin kai harin.

A bangare guda kuma wata kotu ta kungiyar al-Shabab din ta sa an jefe wata mata har ta mutu a kasar , bayan an same ta da laifin auren miji fiye da guda, kamar yadda  wani shafin yada labarai mai alaka da kungiyar ya wallafa.

An tuhumi Shukri Abdullahi Warsame da yin aure sau 11, ba tare da ta rabu da sauran mazajen da ta aura a baya ba.

An tona wani rami da aka saka ta a ciki, inda aka zuba kasa har zuwa wuyanta, kuma mayakan al-Shabab su ka rika jifanta da dutse har ta mutu a garin Sablale da ke yankin Lower Shabelle.