Sojojin Masar Sun Halaka 'Yan Ta'adda 21 A Yankin Sinai
A ci gaba da kaddamar da farmakin da dakarun gwamnatin Masar ke a yankin Sinai, sun sanar da halaka 'yan ta'adda 21 a yankin tare da kame wasu.
Kamfanin dillancin labaran Anatoly ya habarta cewa, rundunar hadin gwiwa tsakanin sojoji da 'yan sandan Masar na ci gaba da kara kaimi a farmakin da suke kaddamarwa kan 'yan ta'adda a Sinai.
Rahoton ya ce tun daga lokacin da aka fara bata kashi tsakanin 'yan ta'adda da kuma dakarun Masar a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, ya zuwa 'yan ta'adda 259 ne aka kashe, yayin da su ma dakarun na Masar guda 259 ne suka rasa rayukansu, tare da kame 'yan ta'adda 4, 467.
Yankin Sinai na kasar Masar dai ya zama wata matattara ta ta 'yan ta'addan Daesh da sauran kungiyoyin 'yan ta'addan wahabiyawa da suke dauke da akidar takfiriyya da suke yaki a sahun kungiyar ta ISIS.