An hallaka 'yan ta'adda da dama a Najeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3079-an_hallaka_'yan_ta'adda_da_dama_a_najeria
Dakarun Tsaron Najeria Sun hallaka Mayakan Boko Haram da dama A jihar Borno
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 28, 2016 11:43 UTC
  • An hallaka 'yan ta'adda da dama a Najeria

Dakarun Tsaron Najeria Sun hallaka Mayakan Boko Haram da dama A jihar Borno

A wata Sanarwa da ya fitar yau, Kakakin Sojin Najeria Kanal Sani Usman ya bayyana cewa a ci gaba da aiyukan tsarkake kasar daga ta'addancin kungiyar boko haram, sojojin kasar sun samu nasarar hallaka mayakan boko haram 25 a yankunan dake cikin kauyukan jihar Borno na arewa maso gabashin kasar

Kanal Sani Usman ya ce baya ga hallaka mayakan na boko haram sojojin sun tsarkake kauyuka guda uku a jihar ta borno, sannan kuma sun ceto fararen hula 18 daga hanun mayakan boko haram din, daga cikinsu 9 kananen yara ne.

Cikin shekaru shidan da suka gabata, duban mutane ne suka rasa rayukansu sanadiyar rikicin boko haram a arewa maso gabashin Najeria, baya ga haka hare-haren kungiyar boko haram ya fadada zuwa kasashen dake makobtaka da Najerian, inda a cikin wadannan kasashen ma aka kashe mutane da dama.