Rasha 2018 : Najeriya Ta Fitar Da Jerin Sunayen 'Yan Wasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30818-rasha_2018_najeriya_ta_fitar_da_jerin_sunayen_'yan_wasa
Mai horas da 'yan wasa na tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr, ya fitar da kwarya-kwaryar sunayen 'yan wasa 30 wadanda daga cikinsu za su buga wa kasar wassani a gasar cin kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni mai zuwa a kasar Rasha.
(last modified 2018-08-22T07:01:50+00:00 )
May 15, 2018 01:18 UTC
  • Rasha 2018 : Najeriya Ta Fitar Da Jerin Sunayen 'Yan Wasa

Mai horas da 'yan wasa na tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr, ya fitar da kwarya-kwaryar sunayen 'yan wasa 30 wadanda daga cikinsu za su buga wa kasar wassani a gasar cin kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni mai zuwa a kasar Rasha.

Daga cikin jerin sunayen 'yan wasan akwai Simeon Nwankwo, na Crotone, wanda ya murza leda sosai Italiya har ma ya zuwa kwallaye bakwai a karawa da Juventus, 

Akwai kuma tsohon dan wasan Chelsea Mikel Obi da Ahmed Musa da Odion Ighalo da Victor Moses da dan wasan nan Lokosa na Kano Pillars.

Ikechukwu Ezenwa da Dele Ajiboye su ne masu tsaron raga guda biyu da Kocin na Najeriya ya zaba.

A cikin wadannan 'yan wasan ne Kocin zai zabi 'yan wasa 23 wadanda za'a tafi dasu Rasha don fafatawa a gasar.

Najeriya dai na daga cikin rukunin D wanda ya kunshi kasashen Croatia da Iceland da kuma Argentina, da zasu buga a gasar da za'a fara a ranar 14 ga watan Yuni idan Allah ya kai.