Ma'aikatan Zimbabwe sun yi watsi da karin kashi 10 kan albashinsu
(last modified Wed, 16 May 2018 05:42:59 GMT )
May 16, 2018 05:42 UTC
  • Ma'aikatan Zimbabwe sun yi watsi da karin kashi 10 kan albashinsu

Kungiyoyin ma’aikata a kasar Zimbabwe sun yi watsi da tayin da gwamnati na karin kaso 10 cikin dari kan albashinsu, bayan da tun farko suna mika bukatar kara musu albashin zuwa ninkin dari bisa dari.

A makon da ya gabata ne  dai shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya amince da karin kashi 10 na albashin ga jami’an soji da ‘yansanda da sauran kananan ma’aikata kafin nan da watan Yuli lokacin da kasar za ta gudanar da zabenta karon farko tun bayan hambarar da gwamnatin Robert Mugabe.

Sai dai kuma a cewar wata kungiya ta musamman da ke wakiltar ilahirin ma’aikatan kasar har yanzu karin na kaso 10 cikin dari ba zai taimaka  ta yadda dubban ma’aikatan za su fice daga kangin talauci ba.

Manyan ma’aikata a Zimbabwe dai na daukar akalla dala 591 yayinda kananan kuma ke daukar dala 253 kowanne wata.

Zimbabwe dai na kashe akalla kashi 90 cikin dari na kowanne kasafin kudinta wajen biyan albashi da kudaden Fansho, sai dai kuma Emmerson Mnangagwa na fatan daidaita matsalar kafin babban zaben kasar wanda  har yanzu ba a sanar da ranar da za a gudanar da shi ba.