Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Palasdinawa A Sudan
Daliban jami'oin kasar Sudan sun gudanar da Zanga-zangar ne a bakin ginin ofishin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Khartum a yau alhamis.
Masu Zanga-zangar sun aike da sako zuwa ga babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress da a ciki suke nuna kin lamintarsu da bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus, wanda su ka bayyana a matsayin cin zarafin al'ummar musulmi.
A ranar litinin din da ta gabata ne dai Amurkan ta dauke ofishin jakadancinta daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus, abin da ya fusata al'ummar musulmi.
Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suna amfani da karfi domin murkushe palasdinawa da suke yin gangamin nuna kin aminicewarsu da matakin na Amurka. fiye da palasdinawa 60 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 3000 su ka jikkata.