'Yan Adawan Nijar Sun Sanar Da Aniyarsu Ta Tattaunawa Da Shugaban Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3094-'yan_adawan_nijar_sun_sanar_da_aniyarsu_ta_tattaunawa_da_shugaban_kasar
'Yan adawa a Jamhuriyar Nijar sun sanar da aniyarsu ta zama teburin tattaunawa da shugaban kasar Mahamadou Issoufou bayan da suka kaurace da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a kwanakin baya.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 29, 2016 00:13 UTC
  • 'Yan Adawan Nijar Sun Sanar Da Aniyarsu Ta Tattaunawa Da Shugaban Kasar

'Yan adawa a Jamhuriyar Nijar sun sanar da aniyarsu ta zama teburin tattaunawa da shugaban kasar Mahamadou Issoufou bayan da suka kaurace da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a kwanakin baya.

Rahotanni daga kasar ta Nijar sun ce 'yan adawan sun sanar da wannan aniyarsu ce bayan tattaunawar da suka yi a jiya Litinin da firayi ministan kasar Brigi Rafini.

Yayin da yake sanar da hakan, Mahamane Malam Sani ,babban sakataren jam'iyyar Moden Lumana ta Hama Amadou, tsohon shugaban majalisar dokokin kasar kuma dan takarar 'yan adawan a zagaye na biyu na zaben ya ce 'yan adawan suna shirye su bude faffadar tattaunawa da gwamnatin kan batutuwa daban-daban da 'yan adawar suka gabatar.

Mahamane Malam Sani, wanda kuma yake magana a madadin gamayyar jam'iyyun adawa ta COPA ya ce suna so ne a tattauna don samo dawwamammiyar hanyar magance abin da ya kira matsanancin halin da kasar take ciki ne.

Shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou wanda ya lashe zaben shugaban da sama da kashi 92%, ya sanar da aniyarsa ta kafa gwamnatin hadin kan kasa inda ya kirayi 'yan adawan da suka kaurace wa zaben da su shigo a dama da su don ciyar da kasar gaba.