An Sako Kananen Yara Sama Da 200 A Sudan Ta Kudu.
(last modified Sun, 20 May 2018 07:55:31 GMT )
May 20, 2018 07:55 UTC
  • An Sako Kananen Yara Sama Da 200 A Sudan Ta Kudu.

MDD ta sanar da cewa 'yan bindiga sun sako kananen yara sama da 200 A kasar Sudan Ta Kudu.

Kakakin Saktare Janar na MDD, Farhan Haq ya ce bayan sako wadannan yara, daga farko wannan shekara ta 2018 da muke ciki, kungiyoyin dake dauke da makamai sun sako kananen yara 806, kuma muna kyautata zaton cewa cikin watani masu zuwa za a sako wasu karin kananen yaran kimanin dubu daya.

A cewar Farhan Haq dukkabin yaran da aka sako daga bangaren kungiyar 'yan tawayen Shaijul-Sha'abi Li Tahriri-Sudan ne , in bada takwas daga Kungiyar  'yan tawaye ta ceton al'ummar kasar.

A shekarar 2011 ne kasar Sudan ta kudu ta balle daga kasar Sudan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama, sannan a shekarar 2013, kasar ta fada cikin rikicin cikin gida bayan da Shugaba Salva Keir ya kori mataimakinsa kuma madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar, kuma ya zuwa yanzu, wannan rikici ya yi sanadiyar salwaltar duban mutane tare kuma da raba kimanin miliyan daya da rabi da mahalinsu.