Ma'aikatar Harkokin Wajen Sudan Ta Kirayi Jakadan Masar Domin Bayyana Masa Kokenta
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta kirayi jakadan Masar da ke kasarta domin bayyana masa rashin jin dadinta kan wani wasan kwaikwayo da za a nuna a wata tashar talabiji na kasar Masar.
A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta fitar yana dauke da cewe: Wata tashar talabiji ta kasar Masar tana shirin fara watsa wani wasan kwaikwayo a cikin wannan wata na ramadana mai suna "Abu-Umar Al-Misri" da ya kunshi yadda wasu 'yan Masar mazauna Sudan suke da hannu a gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar Masar.
Bayanin ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana cewa: Wannan wasan kwaikwayo yana matsayin cin mutunci ne ga al'ummar Masar mazauna kasarta, kuma zai iya janyo matsala a alakar da ke tsakanin kasashen biyu.