Gwamnatin Masar Tana Ci Gaba Da Kame 'Yan Adawar Siyasa
(last modified Mon, 21 May 2018 12:03:00 GMT )
May 21, 2018 12:03 UTC
  • Gwamnatin Masar Tana Ci Gaba Da Kame 'Yan Adawar Siyasa

Mahukunta Masar sun bada umurnin tsare wani dan adawar siyasa kan zargin alaka da kungiyar ta'addanci a kasar.

Jaridar Al-Qudus Arabi ta watsa labarin cewa: Mukhtar Munir lauyan Haitham Muhammadin dan adawar siyasa a Masar ya sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun kama Haitham Muhammadin tare da bada umurnin tsare shi kan zargin alaka da kungiyar ta'addanci a kasar.

Haitham Muhammadin dai ya saba shiga hannun jami'an tsaron Masar, inda a shekara ta 2013 da 2016 aka tsare shi a gidan kurkuku sakamakon shahara da ya yi a fagen nuna adawa da manufofin mahukuntan Masar.

Har ila yau a makon da ya gabata ma mahukuntan Masar sun tsare Shadi al-Ghazali dan adawar siyasar kasar na tsawon kwanaki 15 kan zargin yada labaran karya a shafinsa na sadarwa na twitter da facebook.