Gumurzu Tsakanin Jami'an Tsaron Maurtaniya Da Masu Fataucin Muggan Kwayoyi
Feb 05, 2016 02:11 UTC
Dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Mauriratniya da wasu gungun masu fataucin muggan kwayoyi ya yi sanadiyyar mutuwan jami'in tsaro guda tare da jikkata wasu bakwai na daban.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa; Jami'an tsaron Mauritaniya sun yi dauki ba dadi tsakaninsu da wasu gungun masu fataucin muggan kwayoyi a yankin arewacin kasar lamarin da ya kai ga mutuwar jami'in tsaron kasa daya tare da jikkatan wani na daban.
Majiyar tsaron Mauritaniya ta sanar da jikkata mutane shida daga cikin masu fataucin muggan kwayoyin da suke cikin wata tawagar motoci da suka makare da muggan kwayoyin.
Tags