Burundi : An Yi Na'am Da Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima
(last modified Mon, 21 May 2018 17:19:01 GMT )
May 21, 2018 17:19 UTC
  • Burundi : An Yi Na'am Da Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

A Burundi, sakamakon zaben raba gardama da aka kada kuri'arsa ya nuna cewa mafi yawan 'yan kasar sun amince da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

hakan dai wata dama ce da zata baiwa shugaban kasar, Pierre Nkurunziza, ci gaba da makkale wa kan madafun iko har zuwa shekara 2034, a cewar sakamakon zaben na wucin gadi da aka fitar yau Litini.

Sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar yau, ya nuna cewa 'kashi 73,2 sun amunce da shirin, a yayain da masu adawa dashi suka samu kashi 19,3% na yawan kuri'un da aka kada, sai kuma kashi 3,3 da suka yi rawar kuri'a.

Shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta, Pierre-Claver Ndayicariye, ya ce an samu fitowar jama'a a zaben sosai in kashi 96% na jama'ar da suka cancanci kada kuri'a suka fito zaben.

Tun kafin sanar da sakamakon dai, Jam’iyyun adawa a kasar sun ce ba zasu amince da sakamakon zaben raba gardamar da ya gudana ba akan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, wanda zai baiwa shugaba Pierre Nkrunziza dake shugabancin kasar tun 2005, damar yin wasu wa'adin mulkin shekaru bakwai bakwai har sau biyu daga shekara 2020.