Nijeriya : An Hallaka 'Yan Bindiga 68 A Zamfara
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan 'yan bindiga kimanin 68 da kuma raunata wasu a yayin arangama tsakanin jami'anta da mayakan a jihar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.
kwamandan rundunar sojojin Najeriyar a jihar Sokoto, Udeagbala Kennedy, ya shedawa 'yan jaridu a Gusau, cewa, an kama wasu mutane 6 da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne, sai dai ya ce sojoji 2 sun rasa ransu a lokacin arangama da 'yan bindigar.
Ya ce 'yan bindigar sun kaddamar da hare hare a kauyukan Birane da Bawar-Daji a watannin Fabrairu da Afrilu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 64.
Kennedy ya ce, an fara aikin tarwatsa dukkan maboyar 'yan bindigar da kuma kawo karshe ayyukan maharan a fadin jihar.
Maharan sun kaddamar da hare hare masu yawa a jihar tun a farkon wannan shekarar, duk da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na shawo kan matsalar.