An Kashe 'Yan Ta'adda 3 A Burkina Faso
Ma'aikatar tsaron kasar Burkina Faso ta sanar da hallaka 'Yan Ta'adda uku a wani sumame da jami'an tsaro suka kai maboyarsu dake Ouagadugou babban birnin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto ma'aikatar tsaron kasar Burkina Faso na cewa bayan 'Yan Ta'adda uku, akwai wani soja guda da ya rasa ransa sannan kuma wasu shida na daban sun jikkata daga cikinsu akwai sojoji guda hudu.
Sanarwa tace mutanan da aka kashe su nada alaka da harin da aka kai a watan Maris din da ya gabata a hedkwatar jami'an tsaron kasar da ofishin jakadancin Amurka a babban birnin kasar.
A yayin kai sumamen jami'an tsaron sun samu bidigogi guda shiga da ababe masu fashewa, gami da uniform din sojojin Burkina Faso da na Faransa, tare da wasu wayoyin waya da lawuka da suke da alaka da harin da aka kai a watan Maris din da ya gabata a maboyar 'yan ta'addar.