Alaka Tsakanin Kasashen Habasha Da Saudiyya Tana Ci Gaba Da Yin Tsami
Bayan gwamnatin Habasha ta janye jakadanta daga Saudiyya, a halin yanzu kuma ta kirayi karamin jakadanta a kasar.
Rahotonni sun bayyana cewa: Gwamnatin Habasha ta dauki wannan mataki ne a matsayin maida martani kan jinkirin da mahukuntan Saudiyya suka yi wajen sakin hamshakin attajirin nan dan asalin Habasha mazaunin kasar Saudiyya Muhammad Husaini Al-Amudi.
A makon da ya gabata fira ministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali ya kai ziyarar aikin kwanaki biyu a kasar Saudiyya, inda bayan dawowarsa ya yi furuci da cewa mahukuntan Saudiyya zasu saki Muhammad Husaini Al-Amudi, amma har yanzu babu labarin sakin nashi.
Tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce mahukuntan Saudiyya suke tsare da Muhammad Husaini Al-Amudi kan zargin barnata dukiyar kasa kasancewarsa cikin jerin hamshakan masu kudin kasar ta Saudiyya da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salma ya taso gaba.