An Cimma Matsaya Tsakanin Kungiyar AU Da Turai
Kungiyoyin tarayyar Afirka da na Turai sun cimma yarjejjeniyar daukan mataki na magance matsalolin tsaro, 'yan gudun hijra, samar da ayyukan yi da Noma a kasashen Afirka
Cikin wani bayyani da kungiyar tarayyar Afirka ta sanar, an cimma wannan yarjejjeniyar ne a taron kwamitin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da turai a birnin Brussels ranar larabar da ta gabata.
Sanarwar ta kara da cewa wannan kwamiti zai ci gaba da aiki tare domin samar da sassaucin ra'ayi, ƙarfafa zaman lafiya da tsaro, da kuma gudanar da mulki, ciki har da bayar da tallafin zaman lafiya a Afirka.
Bangarorin biyu sun dauki alkawarin zuba jari a bangaren Noma da kuma kasuwanci, da kuma bangaren ilmin na'ura domin samarwa da matasa ayyukan yi a kasashen Afirka.