An Kaiwa 'Yan Gudun Hijra Hari A Darfur
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31104-an_kaiwa_'yan_gudun_hijra_hari_a_darfur
An Kai hari kan sansanin 'yan gudun hijra uku a yankin Darfur na yammacin Sudan tare da kashe 'yan gudun hijra dake ciki da kuma jikkata wasu na daban.
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 25, 2018 06:27 UTC
  • An Kaiwa  'Yan Gudun Hijra Hari A Darfur

An Kai hari kan sansanin 'yan gudun hijra uku a yankin Darfur na yammacin Sudan tare da kashe 'yan gudun hijra dake ciki da kuma jikkata wasu na daban.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto dakarun hadin gwiwa na MDD da na kungiyar tarayyar Afirka wato  Minuad dake yankin Darfur a jiya Alhamis na cewa tsakanin ranaikun 21 zuwa 23 ga wannan wata na Mayu da muke ciki, an kai hari kan sansanin 'yan gudun hijra guda uku da suka hada da Ardiba,Khamseh Daghigh da Jeddah.

A cewar Dakarun hadin gwiwar na Munuad, wadannan sansanonin guda uku na kumshe da dubunnan 'yan gudun hijira na yankin Tsakiyar Darfur.

Yan gudun hijirar dai sun dora alhakin kai wannan hari ga kungiyar RSF ta wasu mayakan sa kai na kasar ta Sudan da ke goyon bayan gwamnati.

tun daga shekarar 2003 ne yankin Darfur na kasar Sudan ya fada cikin rikici kabilanci.