DRC : Kifewar Kwale-Kwale Ta Yi Ajalin Mutum 50
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31112-drc_kifewar_kwale_kwale_ta_yi_ajalin_mutum_50
Hukumomi a lardin Tshuapa dake yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo, sun ce mutum 50 ne suka rasa rayukansu bayan da wani kwale kwale ya kife a daren ranar Larabar data gabata a tekun Kongon.
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 25, 2018 10:23 UTC
  • DRC : Kifewar Kwale-Kwale Ta Yi Ajalin Mutum 50

Hukumomi a lardin Tshuapa dake yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo, sun ce mutum 50 ne suka rasa rayukansu bayan da wani kwale kwale ya kife a daren ranar Larabar data gabata a tekun Kongon.

Gwanan yankin Mboyo Iluka ya ce, jirgin ruwan wanda ya tashi daga kauyen Monkoto zuwa Mbandaka ya kife ne a lardin Tshuapa.

Kawo yanzu dai ba'a gano musabbabin faruwar hadarin ba.

A cewar wasu majiyoyi daga yankin, tuni aka aike da wata tawaga da ta hada da ministan harkokin ayyukan jin kai, da wasu manyan jami'ai zuwa inda lamarin ya auku domin gudanar da bincike kan wannan batu.

Sai dai a cewar hukumomi, galibi an fi danganta faruwar irin wadannan haddura na kifewar jiragen ruwa a tekun Kongo da rashin ingancin jiragen ruwan ko kuma daukar fasinjoji da suka wuce kima.