An Dage Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Juyin Milki A Burkina Faso
Kotu ta sake dage shari'ar wadanda ake zargi da juyin milki a kasar Burkina Faso
Jaridar Le Jeune Afirka ta nakalto magabatan kotun kasar Burkina Faso na cewa an sake dage shari'ar janar Gilbert Diendéré da abokanisa 83 da ake zarki da yunkurin juyin milki a ranar 16 ga watan Satumbar 2015 zuwa ranar 12 watan yuni mai kamawa.
Rahoton ya ce dukkanin wadanda ake zarki da yunkurin juyin milkin da suka hada da janar Gilbert Diendéré da kuma janar Djibrill Bassolé sun halarta a kotun, to saidai masu kare wadanda ake zargin sun janye saboda wasu dalilai da ba su bayyana ba.
Yunkurin juyin milkin na shekarar 2014 da bai ci nasara a kasar Burkina Faso ya yi sanadiyar mutuwar mutum 14 tare da jikkata wasu 251 na daban.