Najeriya : MDD Ta Taimaka Wa Adamawa Don Yakar Cutar Kwalera
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31168-najeriya_mdd_ta_taimaka_wa_adamawa_don_yakar_cutar_kwalera
Majalisar Dinkin Duniya, ta taimaka wa yankin adamawa dake Najeriya da Dalar Amurka Miliyan biyu don murkushe cutar amai da gudawa ko Kwalera data bulla a yankin.
(last modified 2018-08-22T07:01:53+00:00 )
May 27, 2018 06:13 UTC
  • Najeriya : MDD Ta Taimaka Wa Adamawa Don Yakar Cutar Kwalera

Majalisar Dinkin Duniya, ta taimaka wa yankin adamawa dake Najeriya da Dalar Amurka Miliyan biyu don murkushe cutar amai da gudawa ko Kwalera data bulla a yankin.

kawo yanzu dai mutane a kalla 50 ne cutar ta yi ajalinsu a arewa maso yammacin kasar ta Najeriya tun bayan barkewarta a kashen watan Maris da ya gabata.

Hukumar hana yaduwar annoba a Najeriya ta ce kimanin mutane dubu uku ne suka kamu da cutar ta kwalera a fadin kasar.

Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD, wato OCHA, ya ce yana da fargabar yaduwar cutar a sansanonin 'yan gudun hijira na MDD, a don haka yake bukatar daukin gaggawa domin shawo kan matsalar.