Najeriya : Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutum 4 A Konduga
May 29, 2018 06:51 UTC
'Yan sanda a Najeriya, sun tabbatar da mutuwar mutane hudu sakamakon wani harin kunar bakin wake a garin Konduga dake yankin arewa maso gabashin kasar.
Da yake tabbatar da hakan shugaban 'yan sanda jihar Borno, Damian Chukwu, ya ce, baya ga wadanda suka mutu, da akwai wasu mutum 7 da suka raunana a yayin harin na ranar Lahadi data gabata.
Garin Konduga, dai ya jima yana fama da ire-iren wadanan hare-haren, inda ko a watan Fabrairu da ya gabata, mutum 22 ne suka rasa rayukansu kana wasu 28 suka raunana a jerin hare hare da ake dangantawa dana kungiyar Boko haram.
Tags