An Fara Nuna Damuwa Dangane Da Rikicin Kabilu A Ivory Coast
Wasu daga cikin masu sarautu na gargajiya a kasar Ivory Coast sun fara nuna damuwa dangane da halin da ake ciki a yankunan da ake fama da rikicia tsakanin manoma da kuma makiyaya.
Kamfanin dillanicn labaran Xin Huwa daga birnin Abijan ya bayar da rahoton cewa, masu masarautu gargajiya wadanda kuma suke da tasiri a kan kabilun kasar, sun fara nuna damuwa dangane da yanayin da mutane fararen hula suke ciki a yankin Buna, da ke arewa maso gabashin kasar, sakamakon rikicin da aka yi fama da shi tsakanin manoma da kuma makiyaya.
Wannan rikcii dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 22, da suka hada da jami'an tsaro da kuma manoma da makiya da ma wasu fararen hula na daban, yayin da wasu fiye da 1300 suka tsere zuwa cikin kasar Burkina Faso, wasu dubbai kuma suka fake a sansanonin majalisar dinkin duniya, babbar matsalar da suke fuskanta dai ita ce ta rashin wadataccen abinci da kuma isassun maguguna, musamman ga mata da kuma kananan yara, wadanda su ne suka fi saurin tagayyara a irin wannan yanayi.