Za A Rage Shekarun Tsayawa Takarar Siyasa A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31240-za_a_rage_shekarun_tsayawa_takarar_siyasa_a_najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke cika shekaru 3 akan karagar mulki a wannan Talata,ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zai sanya hannu kan dokar nan ta bai wa matasa damar tsayawa takara nan da kwanaki kadan masu zuwa.
(last modified 2018-08-22T07:01:54+00:00 )
May 29, 2018 14:27 UTC
  • Za A Rage Shekarun Tsayawa Takarar Siyasa A Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke cika shekaru 3 akan karagar mulki a wannan Talata,ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zai sanya hannu kan dokar nan ta bai wa matasa damar tsayawa takara nan da kwanaki kadan masu zuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wani bangare na jawabinsa na bikin Ranar Dimokuradiya da ya gabatar a safiyar wannan talata, inda ya ce nan ba da jimawa ba zai sanya hannu kan sabuwar dokar rage shekarun cancantar tsayawa takarar neman mukaman siyasa, abin da ake ganin zai bai wa dimbin matasa damar shiga a dama da su a zaben shugabancin kasar a shekarar 2019.

A shekarar da ta gabata ce majalisun kasar biyu suka gabatar da kudirin dokar wadda ta bukaci rage shekarun cancantar tsayawa takarar shugaban kasa daga shekaru 40 zuwa 35, yayin da a bangaren gwamnoni da sanatoci aka bukatar rage shekarun daga 35 zuwa 30.

Sai dai a yanzu ana son takaita shekarun neman kujerar mamba a Majalisar Tarayya da ta Jiha zuwa 25.

A bangare guda kuma Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama da gwamnatinsa ta mayar da hankali akai da suka hada da tattalin arziki da cin hanci da rashawa da kuma tsaro.