Nijeriya : Mutum 3 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Ruwan Gombe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31258-nijeriya_mutum_3_sun_rasa_rayukansu_a_ambaliyar_ruwan_gombe
Limamin Masallacin Al-Burma a cikin birnin Gombe na Tarayyar Nigeria da wasu mutane biyu sun rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa da aka yi a yammcin ranar litinin da ta gabata.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
May 30, 2018 02:30 UTC
  • Nijeriya : Mutum 3 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Ruwan Gombe

Limamin Masallacin Al-Burma a cikin birnin Gombe na Tarayyar Nigeria da wasu mutane biyu sun rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa da aka yi a yammcin ranar litinin da ta gabata.

Jaridar Daily Trust ta nakalto wakilinta a jihar Gome yana cewa Limamin masallacin masi suna Malam Mohammad Musa Bello ya rasu ne a kokarin hana ambiyar ruwan tafiya da wata motar daya daga cikin danginsa, amma sai ya nutse cikin ruwan, sannan bayan sa'o'i ukku aka gano gawarsa a karkashin wata gada a unguwar Kumbiya-Kumbiya. 

Banda haka wasu mutane biyu a wasu wurare a cikin birin Sun rasa rasyukansu sanadiyyar amfaliyar ruwan. Hukumar bada agajin gaggawa NEMA a jihar ta Gome ta tabbatar da aukuwar hakan. Sannan shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Jihar SEMA  , Malam Musa Garba ya shaidawa Daily Trust kan cewa ambaliyar ta kashe tabbobi masu yawa da kuma rusa gidaje kimani 20. Sannan ya kara da cewa akwai wasu mutanen da suka bace don haka suna gudanar da bincike don gano cikekken asarorin rayuka da dukiyoyin da ambaliyar ruwan ta shafa.