Fashewar bututun mai ya hallaka mutane 3 a Najeriya
Mutane 3 sun mutu wasu da dama sun jikkata sakamakon fashewar wani bututun mai a yankin Naija Delta dake Najeriya.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Alagu Muriso jami'i a ma'aikatar wannan kamfani na cewa bututun man da ya fashe mallakin Kamfanin hakar mai na Eni na kasar Italiya ne, kuma ya fashe ne a daidai lokacin da ake kan yiwa bututun gyara.
Al’amarin ya auku ne a wani yanki mai suna Olugboboro dake jahar Bayelsa tun ranar lahadin da ta gabata sai dai kuma a jiya litinin aka iya gano gawarwakin mutanen ukun
Kawo yanzu dai babu bayani daga Kamfanin ko bangaren gwamnati kasar game da wannan al’amari.
Saidai tun bayan da kotu ta bayar da Umarnin kame Tampulo tsohon shugaban masu tayar da kayar baya a yankin Neja-delta, ake ci gaba da fuskantar kaiwa bututun Man a Yankin.