An Yanke Daukin Shekaru 14 Ga Tsohon Gwamnan Jihar Taraba
Babbar kotun Najeriya da ke birnin Abuja ta yanke hukuncin dauri a gidan yari kan tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame har tsawon shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba.
Mai shari'a Adebukola Banjoko ya ce kotu ta samu tsohon gwamnan na jihar Taraba da ya yi mulki tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 da laifuka 27 daga cikin 41 da aka tuhume shi da su, sakamakon karkatar da kudi sama da Naira bilyan guda a lokacin da ya ke kan karagar mulki.
Shara’ar ta samo asali ne bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin sa da karkatar da Naira biliyan 1 da miliyan 64 a lokacin da ya rike da mukamin gwamnan Taraba daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Ko da yake an yanke wa gwamnan hukuncin daurin shekaru 14 ne saboda samun sa da laifin karkata Naira miliyan 350 a wani kamfani, Saman Global a cikin makwanni 5 a shekarar 2005, duk da dai Nyame ya ce ba shi da masaniya kan wannan kamfani da ake zance akai.