Rikici A Kasar D/Congo Ya Hallaka Mutane 16
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3130-rikici_a_kasar_d_congo_ya_hallaka_mutane_16
Dakarun tsaron D/Congo sun bayyana da cewa musayar wuta tsakanin Sojoji da 'yan tawayen gabashin kasar ya yi sanadiyar mutuwar Sojoji guda hudu, yayin da a bangaren 'yan tawaye suka kara mutanansu 12.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 29, 2016 22:48 UTC
  • Rikici A Kasar D/Congo Ya Hallaka Mutane 16

Dakarun tsaron D/Congo sun bayyana da cewa musayar wuta tsakanin Sojoji da 'yan tawayen gabashin kasar ya yi sanadiyar mutuwar Sojoji guda hudu, yayin da a bangaren 'yan tawaye suka kara mutanansu 12.

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto Guillaume Dijyek kakakin Rundunar tsaron Kasar D/Congo a jiya Talata na cewa , wannan gumurzu ya faru ne a yankin Empathy mai nisan kilomita 100 daga kudu maso yammacin Goma babban birnin Kivo ta arewa inda aka jima ana fama da rikici.

Kakakin Rundunar tsaron ta Congo ya ce lamari ya auku ne a yayin da Sojojin kasar ke ci gaba da kaiwa 'yan tawayen farmaki domin kwato kauyukan dake hanun 'yan tawayen.

'Yan tawayen kasar Ruwanda dake jibke a kasar D/Congo da ake kira masu fafutukar tabbatar da Democradiya a Ruwanda na fafutukar kafa Gwamnatin 'yan kabilar Tusi. tun bayan kisan kiyashin da aka yiwa 'yan kabilar huti a shekarar 1994 a kasar Ruwanda aka kafa wannan kungiya ta 'yan tawaye.

Akalla Mutane dubu 800 aka kashe Aksarinsu 'yan kabilar Tusi a kisar kiyashin da aka yi na shekarar 1994 na kasar Ruwanda