An Kai Karar Yahya Jammeh Saboda 'Maganin AIDS Na Boge'
Wasu mutane guda uku da suka yi amfani da maganin cutar kanjamau (AIDS) da tsohon shugaban kasar Gambiya Yahaya Jammeh ya samar sun shigar da karar tsohon shugaban bisa zargin ya haifar musu da matsala cikin lafiyarsu.
Kafar watsa labaran Africanews ta ba da rahoton cewa a yau Alhamis din nan ne mutane ukun suka shigar kara a wata babbar kotun birnin Banjul, babban birnin kasar Gambiya inda suka ce amfanin da suka yi da maganin da tsohon shugaba Jammeh ya ce ya samar na cutar AIDS din ya haifar musu da matsaloli a lafiyarsu don haka suke bukatar a bi musu kadi.
Mutane ukun wato Ousman Sowe, Lamin Ceesay da Fatou Jatta suna daga cikin 'yan kasar Gambiyan da aka sanya su cikin shirin maganin cutar AIDS da shugaba Jammeh ya gabatar a shekara ta 2007 inda suka ce an tilasta musu amfani da maganin lamarin da ya kara tsananta rashin lafiyar da suke fama da shi, suna masu cewa wasu daga cikinsu ma sun mutu.
Wannan dai shi ne karon farko da aka kai karar tsohon shugaba Jammeh din wanda ya mulki kasar Gambiyan na tsawon shekaru 22 har zuwa lokacin da aka tilasta masa barin mulki da kuma tafiya gudun hijira a kasar Equatorial Guinea a shekarar bara bayan kayen da ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar.