Burundi : Kotun Tsarin Mulki Ta Yi Na'am Da Sakamakon Zaben Raba Gardama
(last modified Fri, 01 Jun 2018 14:24:11 GMT )
Jun 01, 2018 14:24 UTC
  • Burundi : Kotun Tsarin Mulki Ta Yi Na'am Da Sakamakon Zaben Raba Gardama

Kotun tsarin mulki a kasar Burundi ta tabbatar da sakamakon zaben raba gardama da aka kada kuri'arsa a ranar 17 ga watan Mayu da ya gabata, kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Sakamakon zaben raba gardama da hukumar zaben kasar ta fitar a kwana baya, ya nuna cewa 'kashi 73,24% na al'ummar kasar sun amunce da shirin, wanda zai baiwa shugaban kasar, Pierre Nkurunziza, ci gaba da mulki har zuwa shekara 2034.

Shugaban kotun tsarin mulkin, Charles Ndagijimana, ya ce ba'a samu wasu kura-kurai, da za'a iya cewa sun hadassa cikas a sakamakon zaben ba. 

Kotun tsarin mulkin ta kuma yi watsi da korafin da bangaren jam'iyun hamayya suka shigar a ranar 24 ga wata, kan cewa an tafka kura kurai da kuma zuzuta sakamakaon zaben.

Dama tun kafin sanar da sakamakon zaben, Jam’iyyun adawa a kasar sun ce ba zasu amince da sakamakon zaben ba, akan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, wanda zai baiwa shugaba Pierre Nkrunziza dake shugabancin kasar tun 2005, damar yin karin wasu wa'adin mulkin shekaru bakwai bakwai daga shekara 2020.