Jun 02, 2018 05:32 UTC
  • Rikicin Siyasar Madagascar: Sojoji Sun Yi Barazanar Shigowa Cikin Harkokin Siyasa

Sojojin kasar Madagaska sun yi barazana shigowa cikin harkokin siyasar kasar, watakila da ma kwace madafun iko matukar dai 'yan siyasar kasar suka gagara kawo karshen rikicin siyasar da take faruwa a kasar.

Ministan tsaron kasar Madagaskan, Beni Xavier Rasolofonirina, yayi wannan barazanar inda ya ce lalle sojoji za su iya shigowa cikin harkokin siyasar kasar matukar dai gwamnati da 'yan adawa suka gagara gano mafita cikin gaggawa ga rikicin siyasar da ya ki ci ya ki karewa a kasar.

Tun watan Aprilun da ya gabata ne dai kasar Madagaskan ta shiga cikin wani mawuyacin hali na rikici na siyasa bayan wata gagarumar zanga-zangar da 'yan adawa suka gabatar don nuna rashin amincewarsu ga sabbin dokokin zabe da aka gabatar a kasar wadanda suke ganin an yi hakan ne don 'yan takararsu tsayawa takara a zaben da za a yi shekara mai zuwa.

Duk da cewa a kwanakin baya dai an fara tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawan to amma a halin yanzu tattaunawar ta tsaya cak hakan ne ma ya sanya sojojin yin barazanar kwace madafun iko din.

 

Tags