Al'ummar Kasar Maurtaniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Palasdinawa
Kungiyoyin farar hula a Nouakchott babban birnin kasar Maurtaniya sun gudanar da zanga -zangar goyon bayan masallacin Qudus da kuma al'ummar Palastinu.
Tashar Talabijin din Almayadeen ta kasar Labnon ta habarta cewa a jiya juma'a dubun dubatan al'ummar birnin Nouakchott na kasar Mourtaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan al'ummar Palastinu da kuma masallacin Qudus har zuwa Ofishin jakadancin kasar Amurka, inda suka dinga rera taken yin alawadai da mamayar yahudawan sahayuna da kuma kudirin da shugaba Trump na Amurka ya dauka na mayar da Ofishin jakadancin kasarsa zuwa birnin Qudus.
Sara Ibrahima daya daga cikin limamin masallacin birnin Nouakchott da ya halarci zanga-zangar a hirar da ya yi tare da dan jaridar Almayadeen yayi alawadai kan shuru da Duniya tayi kan ta'addancin mahukuntar haramtacciyar kasar Isra'ila.
A nasa bangare Na'ib Gulam wani dan majalisar dokokin kasar ya bayyana cewa a yau al'ummar birnin Nouakchott sun gwadawa sauran al'ummar kasashen larabawa cewa ba za su sayar da wuraren zarkinsu ba ta hanyar nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da kuma masallacin Qudus mai tsarki.