Shugaba Ouatara Na Son Tsayawa Takara Karo Na Uku
Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Dramane Ouattara ya ce bai kawar da yiyuwar sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku ba a shekara ta 2020.
A yayin da yake hira da jaridar Jeune Afrique,Shugaban kasar Cote D'ivoire Alassane Dramane Ouattara ya cedalilin da ya sanya bayyana hakan, kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi a shekara ta 2016 ya ba shi wannan damar, to sai dai ya ce zai yanke hukunci ne a shekara ta 2020 lura da yanayi na zaman lafiyar kasar ko kuma akasin haka.
Ouattara mai shekaru 76 ya shaidawa Mujallar Jeune Afrique da ake wallafawa a Faransa cewar sabon kundin da za’a fara aiki da shi a 2020 ya baiwa kowa da kowa damar shiga zaben ba tare da sanya shinge ba.
A shekarar 2010 aka zabi Ouattara a wa’adin farko, zaben da ya haifar da tashin hankali lokacin da shugaba Laurent Gbagbo yace ba zai sauka daga kujerar sa ba, duk da kayen da ya sha, wannan mataki da tsohon shugaban kasar ta Cote D'ivoire ya dauka ya janyo rikici da tashin hankali, lamarin da ya salwantar da rayukan mutane da dama.