Dangote Ya Bawa Yansandan Najeriya Mutocin Sintiri 150
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31416-dangote_ya_bawa_yansandan_najeriya_mutocin_sintiri_150
Cibiyar Aliko Dangote Faudation mallakin hamshakin dan kasuwa a tarayyar Nigeria ya bada kyautan motocin sintiri 150 ga hukumar yansandan Najeriya.
(last modified 2018-08-22T07:01:55+00:00 )
Jun 04, 2018 07:27 UTC
  • Dangote Ya Bawa Yansandan Najeriya Mutocin Sintiri 150

Cibiyar Aliko Dangote Faudation mallakin hamshakin dan kasuwa a tarayyar Nigeria ya bada kyautan motocin sintiri 150 ga hukumar yansandan Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Najeria NAN ya nakalto mataimakon shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo yana yabawa shugaban cibiyar Aliko Dangote Alhaji Aliko Dangote a bikin karban motocin. Osinbajo ya kara da cewa wannan ba shi ne karon farko wanda dan kasuwan yake tallafawa al-ummar Nigeria ba. Ya kuma yi kira ga sauran kamfanoni masu zaman kansu da bi sawon Dangote.

Sai kuma a na shi bangaren Alhaji Aloko ya ce cibiyarsa tana tallafawa lamuran da dama a kasar wadanda suka hada da bangaren lafiya hanyoyi da kuma ilmi, sannan a wannan karon ya tallafawa bangaren tsaro ne don ganin irin kalu balan da bangaren yake fuskanta.

Har'ila yau spetan yansandan Najeria Mr Ibrahim Idris ya godewa Dangote da wannan kyautar, ya kuma kara da cewa motocin za su taimaka masu wajen aiwatar da ayyukansu a duk fadin kasar.