Kasashen yankin gabashin Afirka sun fara gudanar da taro a kasar Burundi
Birnin Bujumbura fadar mikin kasar Burundi na karbar bakuncin taron kasashen Gabashin Afrika da manufar fadada alakar dake tsakaninsu.
A jiya ne Talata ce. aka fara taron karo na hudu wanda ya hada magabatan kasashen gabashin Afirka a birnin Bujunbura fadar milkin kasar Burundi.
A yayin buda taron, Joseph Butore mataimakin na biyu ga shugaban kasar Burundi Pierre Nkurinziza ya bayyana cewa irin wannan zama da ya hada magabatan galgajiya da na Gwamnati, shi ne zai kara samar da hadin kai tare da tuntubar juna a tsakanin magabatan gabashin Afirkan.
Taro wanda za a kamala shi a yau Laraba, zai tattauna kan yadda za a magance matsalar Al'umma da kuma tattalin Arzikin yankin.
Mista Joseph Butore ya kara da cewa ko shakka babu, karfafa alaka tsakanin magabatan galgajiya da na Gwamnati tare da ci gaba da tuntubar juna shine babban makami ga magabata na yaki da talauci tare kuma da magance matsalar da Al'umma ke ciki a yanzu.
Kasashen Gabashin Afirkan dai, sun kumshi Burundi, Ruwanda, Kenya, Uganda, Tanzani, Eritrea, Ethipoia, Djibouti, Comoros, Somalia, Sudan ta Kudu da kuma Morris.